IQNA

Guterrs: Duniya Na Bukatar Sulhu Da Zaman Lafiya

14:43 - May 30, 2019
Lambar Labari: 3483686
Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi kira zuwa ga zaman lafiya da sulhu a tsakanin dukkanin al’ummomin duniya.

A cikin wani rutaccen jawabi da ya aike zuwa ga babban taron daliban jami’oin kasashen duniya da ke gudana a kasar Qazagistan wanda aka karanta a gaban taron, babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, bababn abin da al’ummomin duniya ke bukata a halin yanzu shi ne sulhu da zaman lafiya.

Ya ce idan aka yi la’akari da abubuwan da suke wakana a sassa daban-daban na duniya a halin yanzu, na tashe-tashen hankula da yake-yake, hakan babbar manuniya ce a kan cewa duniya na bukatar kawo karshen zubar da jinni da cin zalun.

Haka nan kuam ya yi kira ga matasa musamamn daliban jami’a da suke kan tafarkin neman ilimi, da su amfani da damar da suke da ita wajen da kuma ilimin da suke samu wajen kawo ci gaba ga al’ummomin kasashensu, wanda hakan zai zama babbar gudunmawa daga gare su domin ganin an cimma wannan burin a fitar da duniya daga duhun jahilci da yake-yake.

Taron daliban jami’oin duniya na gudana ne sau daya a kowace shekara, inda masana da kuma cibiyoyi na kasa da kan jagoranci taron, tare da yi wa matasa hannunka mai sanda kan muhimman abubuwan da ke gabansu domin cimma burin ci gaban al’ummomin duniya a dukkanin bangarori.

3815704

 

 

captcha