IQNA

Amurka Na Amfani Da Daesh Domin Cimma Manufofinta A Syria

23:59 - August 29, 2019
Lambar Labari: 3483998
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Rasha ta zargi Amurka da yin amfani da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh domin cimma manufofinta a kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka ce take yin amfani da ‘yan ta’adda a Syria musamman Daesh, domin cimma wasu manufofi a kasar, wanda hakan kuma shi ne musabbabin dukkanin matsalolin tsaro a kasar ta Syria.

Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya ce babu gaskiya  ada’awar da Amurka take kan cewa tana yaki da ‘yan ta’adda a Syria. Maimakon haka ma ‘yan ta’addan suna samun dukaknin taimako da dauki ne daga sojojin Amurka da ke cikin kasar ta Syria, domin kai hare-hare kan jama’a da kuma dakarun gwamnatin kasar ta Syria.

Dangane da batun kasar Afghanistan ma, Lavrov ya bayyana cewa, dole ne Amurka ta zama mai gaskiya idan tana son ganin an samu zaman lafiya  a kasar Afghanistan.

Lavrov ya ce kasarsa a shirye take ta baiwa gwamnatin Afghansitan dukkanin taimako, domin ganin an tabbatar da tsaro da kare rayukan mutane a kasar.

3838394

 

 

 

captcha