Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, Sayyid Abbas Musawi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, kasarsa tana kare hakkokin mata fiye da kowace kasa a yankin gabas ta tsakiya.
Ya ce rahoton na majalisar kungiyar tarayyar turai ko dai ya ginu ne a kan jahilci da rashin sanin hakikanin abin da yake faruwa a kasar dangane da kare hakkokin mata, ko kuma hakan magana ce da take da alaka da siyasa.
Musawi ya ce Iran tana bin tsari ne wanda ya ginu a kan koyarwa ta musulunci, saboda haka duk wani ya ginu a kan wannan mahanga, ba bisa abin da kasashen turai suke kallonsa a matsayin hakkin mata ba, na mayar da su tamkar kayan talla a kamfanonin da nuna tsiraici.
Kasar Iran dai tana wajabta saka tufafi mai rufe jiki ga mata a kasar, a lokaci guda kuma matan suna da hakkin su yi aiki a dukkanin wurare amma da sharadi saka sutura mai rufe jiki da kuma yin lullubi, wanda hakan yasa matan suka samu damar shiga a dama da su a dukkanin bangarori na ayyuka da kuma bincike na ilimi, ta yadda hatta bangaren ayyukan jiragen sama, akwai mata matuka jirgin sama a kasar a halin yanzu.