IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Daukar Mataki Kan masu Zanga-Zanga Da Bindigogi A Iraki

23:14 - October 28, 2019
Lambar Labari: 3484200
Babbar jami’ar MDD a Iraki ta ce masu dauke da bindigogi a cikin zanga-zanga ne suke kashe mutane.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da babbar jami’ar majalisar dinkin duniya kan harokin Iraki Jeanine Hennis-Plasschaert take ganawa da firayi ministan kasa Adel Abdumahd a jiya a birnin Bagadaza, ta bayyana damuwa kan halin da kasar take ciki.

Ta ce bas u goyon bayan duk wani aiki tashin hankali daga kowane bangare, kuma suna goyon bayan jama’a kan bayyana korafe-korafensu amma ta hanyar lumana, ba ta hanyar tashin hankali da lalata dukiyoyi da kaddarorin gwamnati da na jama’a ba.

Haka nan kuma ta bayyana cewa dole gwamnatin Iraki tare da sauran jama’ar kasar su dauki mataki kan mutanen da suke dauke da bindigogi a cikin zanga-zanga, domin hakan baa lama ce ta alahairi ga kasar Iraki ba.

A nasa bangaren Firayi ministan kasar Iraki ya jaddada cewa, gwamnatinsa tana yin iyakacin kokarinta domin aiwatar da dukkanin sabbin sirye-shiryenta na yin gyara domin inganta rayuwar al’ummar Iraki, da kuma yaki da barna da dukiyar kasar, tare da daukar kwararan matakai na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

 

https://iqna.ir/fa/news/3852893

 

 

 

captcha