Kamfanin dillancin labaran iqna, wanann kur’ani an rubuta shi tsakanin karni na 11 zuwa na 13 kuma an ajiye shi a wani wuri na adana kayan tarihi.
Yana da shafuka 867 a cikin bangarori guda 30, kamar yadda aka rarraba juzuoinsa, haka nan kuma yana da nauyi da ya kai kligram 13.
Tun a cikin shekara ta 2007 ce dai aka gyara wannan kwafin kur’ani aka saka shia cikin wani gilashi, wanda dubban mutane da dama suka zuwa wurin suna dubawa a kowace rana a akasar ta China.