IQNA

Musulmin Rohingya Sun Yi Mathabin Da Matakin Da Gambia Ta Dauka

9:16 - December 04, 2019
Lambar Labari: 3484291
Musulmin kasar yamnar sun yi marhabin da matakin da Gambia ta dauka na kai karar gwamnatin Myanmar a kotun duniya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Gwamnatin kasar Gambia ta shigar da kara a hukumance ta hanyar kungiyar OIC a gaban kotun manyan laifuka ta duniya kan kisan kiyashin da aka yi wa musulmin Rohingya a Myanmar.

Cibiyar kare hakkokin Rohingya ta duniya ta marhabin da wannan mataki, kamar yadda su ma musulmin Rohingya suka nuna farin cikinsu da hakan.

Wannan dais hi ne karon farko da wata babbar kungiya wadda ta kunshi kasashe 57 ta shigar da kara kan gwamnatin Myanmar dangane da kisan kiyashin da aka yi wa musulmin Rohingya.

A cikin shekara ta 2017 ce dai mabiya addinin buda gami da sojojin gwamnatin Myanmar suka yi wa musulmi Rohingya kisan kiyashi, inda aka kashe dubbai daga cikin, wasu sama da dubu 700 kuma suka yi gudun hijira zuwa Bangaladesh.

https://iqna.ir/fa/news/3861303

captcha