Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin tashar Russia Today ya bayar da rahoton cewa, a jiya babbar cibiyar bayar da fatawa a Masar ta yi gargadi kan yin amfani da Kalmar ta’addancin musulunci tare da bayyana hakan a matsayin wata hanya ta bakanta fuskar musulunci, da aka fara amfani da ita a 2001.
Cibiyar ta ce babu wani abu ta’addancin musuluci domin kuwa addinin musulunci ba addinin ta’addanci ba ne, saboda haka ba abu ne da za a amince da shi ba a ci gab ada yin amfani da wannan kalma dake danganta ayyukan ta’addanci da musulunci.
Darul Ifta Masar ta ce bayan kai harin 11 Satumba a 2001 ne aka fara yin amfani da Kalmar, sai kuma a harin Madrid 2004, da London 200, da Stockholm 2010, da kuma bayan kirkiro Daesh a 2014.
3861865