IQNA

Jagora: Juyin Juya Hali Jan Layi Ne Ga Shahid Qasim Sulaimani

13:39 - January 08, 2020
Lambar Labari: 3484395
Jagoran juyin juya ya bayyana Shahid Qasim Sulaimani a matsayin gwarzon kare juyin juya halin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a ‘yan sao’in da suka gabata jagoran juyin juya halin musulunci ya gabatar da jawabi a birnin Qom.

Wasu daga cikin abubuwan da jawabin ya kunsa:

 

- Hakan ya kara bayyana imanin al’umma a fili.

- Idanun duniya na kan al’ummar Qom. A ranar 19 ga Dey al’ummar za su fito domin nuna rikonsu da juyin juya halin muslucni.

- Abin da ya faru a ranar 19 ga Dey shi ne, al’umma sun fito domin kare manyan malamansu daga cin zarafi na mahukunta masu girman kai na lokacin, saboda kishin addini.

- A lokacin da mutane suka fito kan tituna suna nuna adawa da zalunci da danniya, a lokacin da aka kara matsa lamba a kansu a lokacin ne suka kara kaimi wanda ya kawo karshen mulkin zalunci.

- Yadda jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen murkushe al’umma, a lokacin ne kuma suka kara kaimi.

- Shahid Sulaimni ya kasance mutum ne gwarzo mai yin amfani da hankalinsa a cikin dukkanin lamurransa, mutum ne mai imani na kololwa, wanda shi ne sirrin nasararsa a cikin lamarinsa.

- Idan babu jarunta da imani da yin amfani da hankali da hikima ba  kama hanyar yin nasara ba.

- Wannan ba a fagen daga na yaki ne ba kawai, har ma a fagen siyasa da jagoranci na al’umma.

- Shadarsa (Qassem Sulaimani) ta tabbatar da cewa juyi na raye

- Haka nan kuma hakan ya sanya ala tilas masu girman kai sun sadda kawunansu kasa, kuam sun gane cewa jamhuriyar musulunci ta Iran ba kanwar lasa ba ce.

- Jiya an harba wasu ‘yan makamai masu linzami, amma wanann ba shi ne abin bukata ba, ba kuma shi ne martani ba, martanin abin da ya far shi ne fitar da sojojin Amurka daga yankin gabas ta tsakiya baki daya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870172

 

 

 

 

 

 

captcha