IQNA

Soke Koyar Da Kur’ani A Makarantun Reno A Sudan

21:48 - January 11, 2020
Lambar Labari: 3484405
Gwamnatin Sudan ta sanar da soke koyar da karatun kur’ani a makarantun Reno.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Umar Alqarai babban jami’i a bangaren tsara manhajar karatun kananan makarantu a Sudan ya ce, gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa, daga yanzu za a daina koyar da kur’ani a makarantun reno a mataki na farko na biyu.

Ya ce bangare na farko shi ne bangaren kananan yara ‘yan shekaru uku zuwa hudu, wadanda wasanni kawai za a rika koya musu, sai kuma bangare na biyu shi ne daga shekara hudu zuwa shida, wadanda za su rika koyon wakoki da yadda ake koyon Magana da harsunan larabci da turanci.

Ya kara da cewa, bayan nan ne yara za su shiga firamare wanda kuma daga nan yanzu za a fara koya ma daliban makarantu karantun kur’ani,a  lokacin sun yi furta haruffan larabci yadda ya kamata.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870650

 

captcha