IQNA

‘Yan Majalisar Dokokin Birtaniya 133 Sun Yi Watsi Da Shirin Yarjejeniyar Karni

23:58 - January 31, 2020
Lambar Labari: 3484469
Bangaren kasa da kasa, yan majalisar dokokin Birtaniya 133 ne suka bukaci Boris Johnson da ya yi watsi da shirin Trump na yarjejeniyar karni.

kamfanin dillancin labaran IQNA, wasu daga cikin yan majalisar dokokin Birtaniya da adadinsu ya kai 133 ne suka bukaci Firayi ministan kasar da ya yi watsi da shirin Trump na yarjejeniyar karni wanda suka bayyana shi da da cewa babu adalci a cikinsa.

Wadannan 'yan majalisa sun bayyana shirin na Trump da cewa yana kunshe da zalunci da danne hakkokin falastinawa a cikinsa.

Haka nan kuma sun bukaci firayi ministan kasar da ya gaggauata daukar matakin yin watsi da wannan batu, domin tabbatar da cewa Birtaniya ba ta zama daya daga cikin masu take hakkokin al'ummar falastinu ba.

Wannan lamari an zuwa ne a daidai lokacin da Birtaniya take shirin ficewa daga kungiyar tarayyar turai a hukumance.

A gobe Asabar ne dai ake sa ran kasar za ta fice daga kungiyar, bayan da aka cimma daidaito tsakanin bangarorin biyu.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875356

captcha