IQNA

Karin Bayanin Darul Ifta Masar Kan Da’awar Cewa An Ambaci Corona A Cikin Kur’ani

23:53 - March 25, 2020
Lambar Labari: 3484654
Tehran (IQNA) cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta mayar da martani dangane da ikirarin da wasu suke kan cewa an ambaci cutar corona a cikin kur’ani.

Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta sanar da cewa, babau gaskiya kan abin da wasu suke fada a shafukan zumunta kan cewa an ambaci Kalmar corona  akur’ani mai tsarki.

Bayanin cibiya ya ce yana da kyau jama’a su rika bin kadun lamurra kamar yadda suke, bai kamata komai a rika jingina shi da kur’ani ba kai tsaye.

Cibiyar ta ce an ambaci nau’oin annoba da kan fadawa wasu al’ummomi da suka gabata, amma babu inda aka mabaci Kalmar cutar corona a cikin kur’ani mai tsarki, kuma wannan da’awa da wasu ke yi ba gaskiya ba ne.

Haka nan kuma cibiyar ta bukaci masana da su rika sanya ido da bin kadun irin wadannan lamurra, wadanda kan karkatar da wasu marassa ilimi daga cikin musulmi saboda rashin sani.

 

3887368

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masar darul Ifta ambaci cutar corona
captcha