IQNA

An Nuna Wani Dadadden Kwafin Kur'ani A Gardaqa Masar

23:39 - June 19, 2020
Lambar Labari: 3484907
Tehran (IQNA) an nuna wani dadden kwafin kur'ani mai sarki a dakin ajiye kayayyaki na garin Gardaqa da ke kasar Masar.

Shafin yada labarai na yaum sai ya bayar da rahoton cewa, a jiya aka nuna wani dadden kwafin kur'ani mai sarki a dakin ajiye kayayyaki na garin Gardaqa da ke kasar Masar wanda ake ajiye ad shi tun shekara 1834.

An yi amfani da salon fasahar rubutu wajen aikin rubutun wannan kwafin kur'ani mai sarki, tare da kayata bangonsa da launuka masu ban sha'awa.

Khalied Ginani shi ne ministan al'adu da tarihi na kasar Masar, ya bayyana wannan dakin ajiye kayan tarihi na Gardaqa yana muhimman abubuwa na tarihi da aka ajiye a cikinsa da suka kai 2000, da suka hada har da wannan kwafin kur'ani.

 

 

3905614

 

captcha