IQNA

Livni Ta Yi Watsi Da Shirin Mamaye Yankunan Falastinawa

22:52 - June 27, 2020
Lambar Labari: 3484934
Tehran (IQNA) Tsohuwar ministar harkokin wajen Isra’ila ta yi watsi da shirin mamaye yankunan Falastinawa a yammacin kogin Jordan.

A zantawarta da tashar CNN ta kasar Amurka, Tzipi Livni ta ce; hankron da gwamnatin Netanyahu ke yi na mamye kashi 30 cikin na yankunan falastinawa da ke gabar yammacin kogin tare da hade su da sauran yankunan Isra’ila, hakan babbar tabargaza ce ta siyasa.

Ta ci gaba da cewa, abin da yake da muhimamnci ne shi ne yin abin da ba zai haifar da wani sabon rikici tsakanin Isra’ila da kawayenta ba, domin kuwa hakan ko shakka babu a cewarta zai haifar ma Isra’ila matsaloli masu tarin yawa, a mataki na yankin gabas ta tsakiya da ma mataki na duniya.

Jam’iyyar Likud ta Netanyahu da sauran jam’iyyun da suke kawance na yahudawa masu tsatstsauran ra’ayi, suna hankoron ganin sun mamaye wasu yankuann Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan a farkon watan Yuli mai kamawa, bayan da suka samu karfin gwiwar yin hakan daga shugaban Amurka Donald Trump.

3906997

 

captcha