IQNA

An Bude Masallacin Nairobi Bisa Sharudda

23:41 - August 21, 2020
Lambar Labari: 3485108
Tehran (IQNA) bayan kwashe tsawon watanni biyar an bude babban masallacin Juma’a na birnin Nairobi na kasar Kenya.

Shafin yada labarai na star ya bayar da rahoton cewa, an bude babban masallacin Juma’a na birnin Nairobi na kasar Kenya bayan kwashe tsawon watanni biyar yana rufe.

An bude masallacin ne bisa wasu sharudda na musamman na kiyaye kaidojin kiwon lafiya, daga ciki kuwa har da yin alwalla kafin zuwa masallaci, da kuma zuwa da darduma.

Haka nan kuma an kayyade adadin mutanen da za su iya yin salla  a cikin masallacin wanda yake daukar masallata dubu 10 a lokaci guda, inda aka sanya dokar cewa mutanen da za su yi salla a ciki a lokaci guda a cikin masallacin kada adadinsu ya wuce dubu daya da 350.

Baya ga wannan kuma an saka sharadin cewa dole ne masallata su bayar da tazarar akalla mita 1.5, sannan kafin shiga cikin masallacin a wanke hannuwa, da kuma saka takunkumin fuska.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya bayyana cewa, za a iya bude wuraren ibada a kasar matukar za su kiyaye sharuddan kiwon lafiya da aka gindaya.

3917856

An Bude Masallacin Nairobi Bisa Sharudda

An Bude Masallacin Nairobi Bisa Sharudda

 

 

 

 

captcha