IQNA

Martanin Falastinawa Kan Kulla Alaka Da Isra’ila Da Bahrain Ta Yi

23:16 - September 12, 2020
Lambar Labari: 3485176
Tehran (IQNA) Gwamnatin Falastinu ta janye jakadanta daga kasar Bahrain, bayan da ta sanar da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

A cikin bayanin Ma’aikatar harkokin wajen Falastinu ta sanar da cewa, ta kirayi jakadan Falastinu da ke birnin Manama a jiya, jim kadan bayan sanarwar da Bahrain ta bayar na kulla alaka tsakaninta da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Bayanin ya ce shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ne da kansa ya bayar da umarnin yin hakan, ya kuma jaddada cewa Falastinu za ta janye jakadanta daga duk wata kasar larabawa da ta sanar da kulla huldar diflomasiyya tare da gwamnatin yahudawa ‘yan mamaya.

Gwamnatin Falastinu dai ta bayyana kulla alaka da Isra’ila da kasashen UAE da kuma Bahrain suka yi a matsayin wani babban cin amana ga al’ummar Falastinu da ma musulmi baki daya., inda suka amince a hukumance da samuwar Isra’ila a matsayin kasa da ta mamaye kasar larabawa ta Falastinu, kuma a haka suka kulla alaka da ita.

Da dama daga cikin masana harkokin siyasar kasa da kasa dai sun yi imanin cewa, babbar manufar hakan dai ita ce, yin amfani da wannan a matsayin wani babban makami na yakin zaben shugaban kasa da Trump ke yi a Amurka, da kuma kokarin tsamo Benjamin Netanyahu daga mawuyacin halin da ya shiga a siyasance a wurin yahudawan Isra’ila.

 

3922282

 

 

captcha