Aikin Umrah Na Farko A Cikin Yanayin Corona
Tehran (IQNA) an fara gudanar da aikin Umrah na farko a cikin yanayin corona, inda mahukunta a kasar Saudiyya suka bayar da dama ga mutane dubu 6 da su gudanar da aikin Umarah, inda mutane 'yan kasar ko kuma mazauna kasar za su iya zuwa su yi aikin Umra su koma gida, kuma ana sa ran za a kara adadin a nan gaba. Haka nan kuma an hana taba hajrul Aswad da bangon dakin ka'abah, kamar yadda ruwan zamzam za a rika bayar da shi ne kawai a cikin robobi.