IQNA

Macron: Kasar Faransa Ba Ta Kiyayya Da Musulunci

22:42 - November 05, 2020
Lambar Labari: 3485337
Tehran (IQNA) shugaban kasar ya bayyana cewa ko alama Faransa ba ta kiyayya da addinin muslunci.

Shafin yada labarai na Arab News ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa ko alama Faransa ba ta kiyayya da addinin muslunci da musulmi

Wannan furucin na zuwa ne a matsayin martani ga wata makala da jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta buga, wadda ke cewa Macron ya goyo bayan matakan yin batunci ga masulucni ne saboda dalilai na siyasa, da kuam neman kuri’ar masu adawa da musulunci a Faransa.

A martanin day a rubuta wa jaridar a jiya Laraba, Macron ya bayyana cewa, ko alama abin da jaridar ta ambata ba gaskiya bane, domin kuwa  a cewarsa Faransa tana girmama musulmi, kuma ba ta adawa da addinin muslunci, kuma maganganun da ya yi yana nufin masu tsatsauran ra’ayi ne daga cikin msuulmi wadanda suke ayyukan ta’addanci da sunan addinin musulunci.

Macron ya fuskanci akkausan martani daga musulmi a ko’ina a cikin fadin duniya, inda hakan ya kai ga muuslmi sun fara kauracewa sayen kayayyakin Faransa, inda ala tilas Macron ya fito ya janye kalamansa na batunci ga addinin muslunci.

 

3933397

 

 

 

captcha