IQNA

An Cafke Paludan Mai Tsananin Kiyayya Da Musulunci

23:36 - November 13, 2020
1
Lambar Labari: 3485362
Tehran (IQNA) mutumin nan dan kasar Danmark mai tsananin kiyayya da addinin muslunci Rasmus Paludan ya fuskani matsala a wasu kasashen turai tare da hana shi kona kur’ani.

Rahotanni sun ce kasashen turai sun fara daukar matakai na ba sani ba sabo a  kan Rasmus Paludan dan kasar Danmark mai tsananin kiyayya da addinin muslunci, wanda a baya yake yawo a kasashe daban-daban yana gudanar da gangamin kona kur’ani mai tsarki a bainar jama’a.

A ranar Laraba da ta gabata ya kudiri aniyar gudanar da gangamin kona kur’ani mai tsarki a yankin Sharl de gol da ke birnin Paris na kasar Faransa, amma jami’an tsaron kasar Faransa suka cafke shi, kuma suka fitar da shi daga kasar.

Bayan nan Paludan ya nufi kasar Belgium, inda shi da mutanensa suka  yi nufin gudanar da wani gangamin na kona kur’ani a yankin Molenbeek-Saint-Jean da ke cikin gundumar Brussels fadar mulkin kasar.

Mahukuntan kasar ta Belgium sun dauki matakin kame shi tare da mutanen nasa wadanda suka shigo cikin kasar da wannan manufa, kuma fitar da su zuwa kasar Danmark a daren jiya, kamar yadda kuma hukumomin Belgium suka haramta musu shiga cikin kasar har tsawon shekara guda.

Kafin wannan lokacin dai Paluda ya jagoranci gangamin kona kur’ani mai tsarki a wasu kasashen turai.

 

3934891

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Nura musa yakasai
0
0
Allah yakara taimakon addinin musulunci amin
captcha