IQNA

Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Birnin Jidda Na Saudiyya

23:41 - November 13, 2020
Lambar Labari: 3485364
Tehran (IQNA) kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a makabartar wadanda ba musulmi ba a birnin Jidda.

Shafin yada labarai na Al-nashra ya bayar da rahoton cewa, kungiyar ‘yan ta’addan Takfir na Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a makabartar wadanda ba musulmi ba a birnin Jidda da ke kasar Saudiyya.

An kai harin ne dai a lokacin da ake gudanar da wani taro na tunawa da kawo karshen yakin duniya na daya, wanda jakadun kasashen turai da suka hada har da na Faransa suka halarci wurin, inda mutane suka jikkata.

Faransa ta yi Allawadai da harin, tare da kiran mahukuntan Saudiyya da su gaggauta gano dukkanin wadanda suke da hannu a wannan hari domin hukunta su.

A kowace ranar 11 ga watan Nuwamba kasashen turai na daukar ranar a matsayin ranar kawo karshen yakin duniya na daya.

 

3934852

 

 

captcha