IQNA

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Musulunci A Iran:

Makiya Ba Su Da Karfin Gwiwar Yin Shishigi A Kan Jamhuriyar Musulunci

21:25 - November 26, 2020
1
Lambar Labari: 3485401
Tehran (IQNA) Janar Hussain Salami ya bayyana cewa yaki da kasar Iran ya fita daga cikin jerin zabin da makiyan kasar suke da shi.

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran (IRGC) Burgediya Janar Hussain Salami ya bayyana cewa, yaki da kasar Iran ya fita daga cikin jerin zabin da makiyan kasar suke da shi, domin fuskantarta.

Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci ta kasar Iran ta nakalto Salami yana fadar haka a jiya Laraba a lokacin da yake jawabi a taron hotunan bidiyo na zagayowan ranar kafa rundunar mayakan sa-kai ta Basij a nan Tehran.

Salami ya kara da cewa dakarun Basij sun taimaka sosai wajen kare kasar Iran daga makiyanta tun bayan kafata shekaru fiye da 40 da suka gabata, sannan suna taimakawa wajen ayyukan ci gaban kasa a bangarori da dama.

Har’ila yau a yau Burgediya Janar Husain Salami ya kaddamar da wasu shirye-shirye na kyautata ayyukan dakarun sa kai na Basij. A rana irin ta yau ce shekaru kimanin 40 da suka gabata Imam Khomaini  ya bada umurnin kafa dakarun sakai na Basij.

3937387

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Kabiru muazu
0
1
Muslim tawuce wasa a duniya
captcha