IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Na'am Da Ayyana Lokacin Gudanar Da Zabe A Palestine

18:16 - January 17, 2021
Lambar Labari: 3485563
Tehran (IQNA) majalisar dinkin duniya ta yi na'am da matakin da Mahmud Abbas ya dauka na ayyana lokacin zabe a Falastinu.

Kakakin babban sakataren majalisar dikin duniya   Stephane Dujarric ya bayyana cewa, Antonio Guterres ya bayyana jin dadinsa matuka da ayyna lokain gudanar da zabukan Falastinu da Mahmud Abbas ya yi.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya bayyana cewa za’a gudunar da manyan zabuka a Falasdinun a tsakiyar wannan shekara da muke ciki.

Za’ayi zaben ‘yan majalisar dokokin da kuma na shugaban kasa a ranakun 22 ga watan Mayu da kuma 31 ga watan Yulin 2021.

Karo na farko kenan da zabe zai gudana a yankin Falasdinawa cikin sama da shekaru 15.

Rashin gudanar da zaben dai yana da nasaba ne da sabanin dake akwai tsakanin Falasdinawan Jam’iyyar Fatah ta Mahmoud Abbas, da kuma kungiyar Hamas.

Jam’iyyar Fatah ta Mahmoud Abbas ita ce ke rike da iko da yammacin kogin Jordan, yayin da kungiyar Hamas ke rike da yankin Gaza.

Amma a watan Satumban bara bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar hadin gwiwa, da kuma gudanar da zabukan.

Tuni dai Kungiyar tarayyar turai ta bukaci Isra’ila data taimakawa Falasdinun wajen gudanar da zabukan masu zuwa.

3948242

 

captcha