IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali na Iran Ya Ziyarci Makabartar Shahidan Juyi

Tehran (IQNA) jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya ziyarci makabartar da aka bizne wadanda suka rasa rayukansu a gwagwarmayar juyin juya hali.

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ziyarci makabartar da aka bizne wadanda suka rasa rayukansu a gwagwarmayar juyin juya halin muslunci a  kasar shekaru 42 da suka gabata, inda ya yi karatun kur'ani da kuma addu'oi  a gare su.