IQNA

Guterres: Nuna Wariya A Tsakanin ‘Yan Adam Ya Kawo Babban Ci Baya Ga Al’ummomin Duniya

21:24 - February 25, 2021
Lambar Labari: 3485688
Tehran (IQNA) Babban sakataren majalisar dinmin duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, nuna wariya  a tsakanin ‘yan adam ya kawo babban ci baya ga harkokin al’ummomin duniya.

Guterres ya bayyana hakan ne a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na twitter, inda ya bayyana cewa, ana samun karuwar nuan kyama a tsakanin mutane saboda dalilai da dama, da suka hada na banbancin addini ko akida ko kabila ko kuma jinsi da makantan hakan.

Ya ce a dukkanin bangarorin abu ne mai matukar muni a tsakanin bil adama, kuam nauyi ne da ya rataya a kan mahukunta da masu karfin fada a ji a tsakanin kowace al’umma, su dauki matakin kawo karshen irin wannan dabi’a a tsakanin al’ummominsu, yin hakan shi ne zaman lafiyar duniya.

Ya yi ishara da yadda musulmi a wasu bangarori na duniya  suke fuskantar matsaloli na nuna musu wariya har da kyama da sauran ayyuka na cin zarafi, kamar yadda mabiya addinin kirista ma suna fuskantar irin hakan a wasu bangarorin, wanda dukkanin hakan abu ne da bai dace ba.

Dangane da bullar cutar corona kuwa, ya bayyana cewa hakan shi ma ya haifar da wasu matsalolin na zamantakewa a kasashen duniya da dama, musamman cin zarafin mata, wanda dukkaninsu abubuwa da ya kamata a hada karfi da karfe domin ganin bayansu a tsakanin al’ummomin duniya.

3956173

 

captcha