IQNA

‘Yar Majalisar Dokokin Amurka Musulma Ta Ce An Gina ‘Yan Sandan Kasar Ne BISA Nuna Banbanci Da Wariya

23:46 - April 14, 2021
Lambar Labari: 3485809
Tehran (IQNA) ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta bayyana cewa an gina tsarin rundunar ‘yan sandan kasar ne bias nuna banbnci da wariya.

Shafin jaridar Quds Al-arabi ya bayar da rahoton cewa, Rashida Tlaib ‘yar majalisar dokokin Amurka musulma ta bayyana cewa an gina tsarin rundunar ‘yan sandan kasar ne bias nuna banbnci da wariya a tsakanin al’ummar kasar.

Rashida ta bayyana hakan ne sakamkon kisan wani matashi bakar fata dan shekaru 20 da haihuwa da ‘yan sanda suka yi a garin Mineapolis a cikin wannan mako.

Ta ce ba abu ne mai saukia  iya gyara akidar ‘yan sanda Amurka ta nuna wariya da banbanci da kin jinin wani jinsia  tsakanin al’ummar amurca ba.

Rashida Tlaib wadda ‘yar asalin Falastinu ce da take zaune a Amurka, tana wakiltar jihar Michigan ne a majalisar dokokin Amurka, inda ta lashe wannan kujera har sau biyu a jere.

Ko lokutan baya an samu irin wannan matsala a wanann gari, inda dan sanda ya take wuyan wani bakar fata har sai da ya kashe shi har lahira.

 

3964384

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wuyan bakar fata jihar Michigan wakiltar
captcha