IQNA

Rauhani: Masu Nuna Damuwa Kan Tace Sanadarin Uranium Kashi 60% Da Iran Ta Fara Yi Suna Yin Kure

23:37 - April 16, 2021
Lambar Labari: 3485813
Tehran (IQNA) shugaba Rauhani ya bayyana cewa Za Mu Iya tace sanadarin urani’um da darajar da za ta kai 90%, amma ba manufarmu ce mu kera makaman nukiliya ba.

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ne ya bayyana cewa; Za Mu Iya tace sanadarin urani’un da darajar da za ta kai 90%, amma ba manufarmu ce mu kera bam na din Nukiliya a shirin namu ba.

Shugaban kasar ta Iran wanda ya bude wasu manyan ayyuka guda hudu na tantance dangogin man fetur a yau Alhamis ta hanyar bidiyo daga nesa, ya kuma yi watsi da damuwar da Amukra da kasashen turai uku su ka nuna saboda yadda Iran din ta kai darajar urani’um din da take tacewa zuwa 60%.

Shugaban na kasar Iran ya zarge su da cewa su ne su ka ja Iran din take daukar matakan da take dauka a wannan lokacin, amma da zarar sun koma kan aiki da yarjejeniyar, to Iran din za dakatar da tace Uranium da daraja 20% da kuma 60%.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma fadawa Amurka da kasashen turai din cewa; Iran tana son cin moriyar fasahar Nukiliya ne ta ruwan sanyi, amma ku ne wadanda su ke kera makaman Nukiliya tun shekaru da dama, kuma kuke girke su da adana su, sannan a kowace shekara kuke kara kera wasu sabbi.”

3964757

 

 

 

captcha