IQNA

Wasu Sabbin Sharuddan Saudiyya Kan Ayyukan Umrah

21:05 - July 28, 2021
Lambar Labari: 3486147
Tehran (IQNA)Gwamnatin kasar Saudiyya ta kara saka wasu sharudda ga masu ziyara na ayyukan ibada na Umrah daga kasashen ketare.

Kafofin yada labaran Saudiyya sun bayar da rahotannin cewa, mataimakin ministan ma’aikatar aikin hajji da Umra ta kasar Saudiyya Hesham saeed ya sanar da cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki na karuwar barazanar cutar corona, sun kara wasu sharudda ga masu zuwa Umrah daga kasashen ketare.

Ya ce a halin yanzu akwai kasashen da gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa ‘yan wadannan kasashen ba za su iya zuwa kasar Saudiiya ba saboda dalilai na kiwon lafiya.

Ya ce wadanda suke bukatar zuwa aikin umrah daga wadannan kasashen, za su iya neman izinin shiga cikin kasar Saudiyya, daga kasashen da aka yarje musu shiga cikin kasar.

Ya ce hakan ya hada da neman visa da kuma tabbatar da cewa an samu rigakafin cutar corona na’in rigakafin da gwamnatin Saudiyya ta amince da shi a hukumance kafin shiga kasar.

Baya ga haka kuma, daga cikin sharuddan shi ne dole ne duk wanda ya shiga kasar, a duk lokacin da ya yi aikin ibada na Umrah, bayar ziyartar dakin Ka’abah da sa’io 6, dole ne ya kai kansa wajen jami’an kiwon lafiya, domin bincikar lafiyarsa.

3987064

 

 

captcha