IQNA

Kungiyoyin Musulmin Amurka Sun Karrama Ilhan Omar Saboda Kare Musulunci Da Take A Majalisa

23:10 - December 04, 2021
Lambar Labari: 3486642
Tehran (IQNA) Kwamitin musulmin Amurka ya yabawa Ilhan Omar ‘yar Majalisar Musulma bisa irin hidimar da take yi wa al’ummar Musulmi a kasar.

A rahoton da shafin mujallar Hill ya bayar, a yau Asabar Ilhan Omar, ‘yar majalisa musulma, za ta samu lambar yabo a wani buki da kungiyar musulmin Amurka ta shirya tare da karrama ta a matsayin babbar Musulma mai hidima a kasar ta Amurka.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR mai rajin kare musulmi a kasar Amurka ta bayyana cewa Ilhan Omar za ta samu lambar yabo ta aikin da ta yi a majalisar dokokin Amurka, musamman ganin rashin jituwa tsakaninsa da Laurent Bubert, dan majalisar wakilai mai tsananin kiyayya da musulunci, da kuma yadda ta kalubalance shi wajen kare musulunci daga batuncin da wannan dan majalisa yake yi.
 
CAIR ta bayyana cewa Ilhan Omar ta cancanci kyautar ne saboda jajircewarsa wajen yin hidima da jajircewarta wajen fuskantar kyamar ‘musulunci yan majalisar dokokin kasar Amurka.

A cikin wani faifan bidiyo wanda aka yi ta yin  Allah wadai da shi, Bobert ya yi izgili da cewa Ilhan Omar 'yar ta'adda ce, Kalaman da suka haifar da cece-kuce kan lamarin.

Shugabannin jam'iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka sun fitar da wata sanarwa inda suka bukaci Bobert da ya janye kalaman nasa, kuma ya guji maimaita irinsu.

Cibiyar ta CAIR ta fitar da wata sanarwa a makon da ya gabata inda ta kira kalaman Bobert a matsayin abin kyama tare da yin kira ga Majalisa da ta yi Allah wadai da dan majalisar, amma har yanzu Majalisar wakilan Amurka ba ta dauki matakin yin Allah wadai da Bubert ba.

 
 

4018222

 

 

captcha