IQNA

Baje Kolin Kur'ani Mai Taken (Nun Wal Qalam) A Kasar Iraki

21:24 - December 28, 2021
Lambar Labari: 3486742
Tehran (IQNA) za a bude wani baje kolin ayyukan fasaha na kur'ania karon farkoa yankin Kirkuk na kasar Iraki mai taken (Nun wal Qalam)

Kamfanin dilalncin labaran iqna daga kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, za a fara baje kolin ne a ranar gobe Laraba 29 ga watan Disamba 2021 a filin wasanni na Kirkuk da ke kan titin Bagadaza, kuma za a ci gaba da shi har zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2022.

Cibiyoyin al'adu da hukumar wayar da kan al'ummar Iraki (North Axis Command) za su hada kai wajen gudanar da wannan baje kolin, wanda zai kunshi bangarori daban-daban da suka hada da baje kolin ayyukan kur'ani, littafai, nuna na'urorin dijital, nano, sana'o'in hannu da yara da matasa suke samarwa.

Za a bude wannan baje kolin ne tare da halartar manyan jami'an kasar Iraki da jami'an yankin a birnin Kirkuk, kuma an gayyaci 'yan kasar ta Iraki da su halarta.

 

4024047

 

 

 

captcha