IQNA

​An gudanar da taron karatun kur'ani mai tsarki a Madagaska ga ruhin Qassem Soleimani

21:11 - January 11, 2022
Lambar Labari: 3486806
Tehran (IQNA) karatun kur’ani mai tsarki ga ruhin Qassem Sulaimani da Abu mahdi al-Mohandes a Madagaska

A madadin cibiyar  Ahlul Baiti (AS) da ke kasar Madagaska, an gudanar da taron karatun kur'ani mai tsarki na tunawa da cika shekaru biyu da shahadar Soleimani da Abu Mahdi al-Mohandes da 'yan uwansu tare da halartar malamai.

A yayin wannan taron da aka gudanar a tsakiyar birnin Tahoora a lardin Antananarivo, an yi karatun kur’ani mai tsarki ga ruhin Soleimani, da Abu Mahdi Al-Mohandes, da kuma marigayi Sheikh Abdulkarim da marigayi Sheikh Adam.

Babban malamin cibiyar Ahlul-Bait (AS) a kasar Madagascar, ya karanta sakon ta'aziyya Hojjatoleslam Mohammad Javad Zarean, mataimakin shugaban cibiyar Ahlul-Bait (AS) ta duniya.

4027729

 

 

 

captcha