KUFA (IQNA) – Masallacin Kufa ko kuma babban masallacin Kufa na daya daga cikin masallatai masu dimbin tarihi a duniyar Musulunci da ke da tazarar kilomita 12 daga arewacin birnin Najaf na kasar Iraki.
Masallacin ya kasance gidan Imam Ali (AS) kuma yana dauke da kaburburan fitattun mutane irinsu Muslim ibn Aqeel, Hani ibn Urwa, da Al-Mukhtar.