Masu ziyara daga kasashen waje sun yi taron Maulidin Imam Hadi (AS) a Hubbaren Imam Ridha (AS)
IQNA – Daruruwan masu ziyara daga kasashen waje ne suka halarci taron maulidin Imam Hadi (AS) a hubbaren Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad a ranar 21 ga watan Yunin 2024.
An haifi Imam Hadi (AS), limamin Ahlul baiti na goma, a shekara ta Hijira ta 212 a Madina. Ana bikin zagayowar ranar haihuwarsa a kowace shekara.