IQNA

Babban sakataren kungiyar Hizbullah zai yi jawabi a yau Juma'a

19:42 - December 04, 2025
Lambar Labari: 3494295
IQNA - Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, zai yi jawabi a ranar Juma'a ta wannan makon kan taron tunawa da malaman da suka yi shahada a hanyar Kudus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Manar cewa, a cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa: Sheikh Naim Qassem babban sakataren kungiyar Hizbullah zai yi jawabi a ranar Juma'a 4 ga watan Disamba a wani bukin da kungiyar Hizbullah ta shirya na tunawa da malaman da suka yi shahada a kan hanyar zuwa birnin Kudus.

An yi wannan buki ne domin karramawa da kuma tunawa da wadanda suka hada girman ilimi da daukakar shahada a cikin su. Shahidai da haskensu ya cika da shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, Sayyidi Shahidai na kasa, da Sayyid Hashem Safi al-Din.

Za a gudanar da bikin ne a ranar Juma'a da karfe 14:30 agogon birnin Beirut a hubbaren Sayyid Hassan Nasrallah da ke yankin kudancin birnin Beirut.

 

 

4320778/

 

captcha