IQNA

9:00 - January 13, 2014
Lambar Labari: 1358111
Bangaren siyasa, A safiyar yau Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban malamai, daliban makarantar hauza da sauran mutanen garin Qum don tunawa da zagayowar shekaru talatin da shida da yunkurin 19 ga watan Dey na mutanen garin nan Qum.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar daya daga cikin bangarori masu muhimmanci na yunkurin 19 ga watan Dey na shekarar 1356 (hijira shamsiyya) shi ne gudanar da aiki tare da dogaro da imani da basira sannan a lokaci mafi tsanani inda ya ce: Mafi muhimmancin darasin da ke cikin yunkurin 19 ga watan Dey na mutanen Qum shi ne cewa a lokacin da ake son tsallake duk wata matsala, to wajibi ne a shigo fage tare da tsayayyen imani da basira da fahimtar makiyi da kuma rashin mance irin kiyayyar da ya nuna, haka nan kuma da dogaro da irin karfi da kwarewar da al'umma da matasa suke da shi, sannan da kuma rashin dogaro da ‘yan kasashen waje.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da ayar nan ta Suratul Rum da take nuni da cewa Allah ya dauki taimakon muminai a matsayin wani nauyi da ke wuyansa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wannan alkawari na Ubangiji da ke cikin wannan ayar yana da alaka ne da lokacin da muminai suka zamanto ba su da komai kashin fata na samun nasara a gaban makiya. Don haka a wancan ranar da al'umma, matasa da daliban makarantar hauzar Qum suka fito kan tituna don kare marigayi Imam Khumaini (r.a) da gagarumin yunkurinsa na fada da dagutu inda aka zubar da jininsu, babu wani da yake zaton cewa wannan yunkurin zai haifar da irin wannan gagarumin tasirin. Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar dai karfafaffen imani ya hadu da basira da aiki a lokacin da ya dace bugu da kari kan tsayin daka, to kuwa ko shakka babu taimakon Ubangiji zai zo.

Jagorn juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Idan har a wani waje muminai suka rasa irin wannan taimako na Ubangiji, to kuwa hakan ta faru ne ko dai sakamakon raunin imaninsu ko kura-kuransu ko kuma imaninsu ba tare da basir ba. Don kuwa rashin basira tamkar rashin ido ne. Mutumin da ba shi da idanuwa, to ba zai iya gane hanya ba don haka sai ya bace.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Wannan shi ne dalilin da ya sanya nake ta magana kan wajibcin nuna basira.

Jagoran ya bayyana cewa rashin wasu sharuddan samun taimako na Ubangiji su ne dalilan da suka sanya wasu al'ummomi fuskantar rashin nasara a yayin da suka yunkura inda ya ce: Al'ummar Iran sun sami nasarar samar da dukkanin wadannan sharuddan da suka hada da karfafaffen imani, basira, aiki a kas da kuma tsayin daka, don kuwa sun sami shiryarwa ta gaskiya irin ta marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda ya kasance masani wanda ya san inda duniya ta sa gaba, masanin addini wanda kuma ya yi watsi da son duniya da amfani da kashin kai.

Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin dubi da tuntuni cikin abubuwan da suka faru a baya don daukar darussan daga karfi ko kuma raunin da ake da shi, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Bai kamata wani ya yi tunanin cewa makiya juyin juya halin Musulunci sun janye daga irin wannan kiyayyar da suke nunawa ba.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Mai yiyuwa ne a iya tilasta wa kowane irin makiya ja da baya daga kiyayyar da yake nunawa, to amma bai kamata a gafala daga makiya da sansanin makiyan ba, kamar yadda kuma bai kamata a yaudaru daga sakin fuskar makiya ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar koda wasa bai kamata a mance da manufar da aka sa a gaba ba inda ya ce: Manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce isa ga koyarwar Musulunci, wato samar wa dan'adam da ci gaba na duniya da lahira. Ba za a iya kai wa ga wannan manufa mai girma ba kuwa in ba ta hanya karfafaffen imani da nuna basira cikin lamurra da kuma rashin gafala daga makiya ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Dalilin da ya sanya a lokuta da dama na ke fadin cewa makomar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wata makoma mai kyau da faranta rai shi ne cewa al'ummarmu tana da imani, basira da kuma fahimtar makiya kamar yadda kuma take da ruhi da karfin gwiwa na aiki da samar da sabbin abubuwa.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wani lamari ne wanda matasanmu suka kutsa cikinsa sannan suka gaza samun nasara a cikinsa. Duk wata matsalar da ta kutso kai, idan har matasanmu suka kutsa cikinsa, to kuwa za su yi nasara kansa. Hakan kuwa albarkacin irin kwarewa da karfin da Allah Madaukakin Sarki ya arzurta su da shi ne.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kiran da nake yi ga jami'an gwamnati shi ne cewa su dogara da karfi na cikin gida wajen magance duk wata matsalar da ta kunno kai, kada su damfara fatansu ga kasashen waje.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Wajibi ne dukkanin fatanmu ta dogara ga taimako na Ubangiji da kuma karfin da muke da shi a cikin gida. Hakan kuwa shi ne yake ba wa wannan kasa ta mu lamuni.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da kuskuren da makiya suke yi wajen rashin kyakkyawar fahimtar al'ummar Iran inda ya ce: A yau makiyanmu suna magana tamkar ka ce al'ummar Iran ta mika wuya da yin saranda saboda matsin lamba da takunkumin da aka sanya mata, alhali kuwa kuskure suke yi. Don kuwa wannan al'umma ta mu ba al'umma ce wacce za ta yi saranda a gaban makiya ba.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar a baya ma a lokacin da al'ummar ta shiga cikin matsalar da tafi irin wannan matsalar ba ta mika kai ba inda ya ce: Babbar misalin da babu wani da ya isa ya musanta shi ne kallafaffen yaki na shekaru 8 da aka kallafawa Iran, a lokacin da dukkanin ma'abota karfi na duniya sun kasance suna taimaka wa Saddam don ya cutar da al'ummar Iran. To amma duk da haka Allah Madaukakin Sarki ya taimaka wa al'ummar Iran sakamakon imani da tsayin dakan da suka yi na fitowa fagen daga da dogaro da irin karfin da suke da shi. Haka suka ta samun nasara bayan nasara, sannan kuma suka tilasta wa gwamnatin Ba'ath (ta Iraki) da masu goya mata baya ja da baya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A yau ma hanyar magance matsalolin da ake fuskanta ita ce tsayin daka wajen tinkarar makiya ta hanyar dogaro da Allah Madaukakin Sarki da kuma irin karfin da ake da shi.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A lokacin da makiya suka fuskanci wata al'umma ma'abociyar tsayin daka, to ba su da wata mafita face ja da baya. Don haka wannan tunanin na cewa al'ummar Iran sun zauna teburin tattaunawa da (manyan kasashen duniya) ne sakamakon takunkumi da matsin lambar da suke fuskanta, lalle hakan babban kuskure ne. Ko shakka babu al'ummar Iran za su tabbatar wa da duniya rashin ingancin wannan tunani na makiyan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: A baya ma mun sanar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta tattauna da wannan Shaidaniyar (Amurka) cikiin wani batu na musamman da take ganin akwai maslaha cikin hakan don kawar da sharrinta.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar daya daga cikin albarkokin wannan tattaunawa ta baya-bayan nan shi ne bayyanar wa da duniya irin kiyayyar da jami'an Amurka suke yi da Iran da kuma al'ummar Iran da kuma Musulunci da musulmi, wanda ake iya ganin hakan cikin maganganu da ayyukan jami'an Amurka daban daban.

Jagoran ya ce: Dalilin da ya sanya Amurka suka gaza kawo wa Iran hari, shi ne cewa raunin da suke da shi ba wai saboda ba sa kiyayya da al'ummar Iran ba. Su da kansu suke fadin cewa idan da za mu iya da mun kawo karshen shirin nukiliyan Iran, amma ba za mu iya ba. Na'am lalle ba za su iya. Don kuwa al'ummar Iran sun kuduri aniyar tsayawa da kafafunsu da kuma shigowa da irin karfi da kwarewar da suke da ita cikin fage.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Tattaunawar baya-bayan nan ta tabbatar da kiyayyar da Amurka take yi da al'ummar Iran da kuma irin raunin da take da shi.

Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da ci gaba da nuna kiyayyar da ‘yan siyasar Amurka da kafafen watsa labaransu suke nuna wa Jamhuriyar Musulunci da kuma al'ummar Iran musamman dangane da batun take hakkokin bil'adama da suke cewa ana yi a Iran, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Idan har wani zai yi magana kan hakkokin bil'adama, to bai kamata Amurkawa su yi magana ba, don kuwa gwamnatin Amurka ita ce babbar mai take hakkokin bil'adama a duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da irin goyon baya ido rufe da Amurka take ba wa haramtacciyar kasar Isra'ila da irin zalunci da ashararancin da take yi a kan al'ummar Palastinu musamman ga mutanen Gaza ta hanyar hana isar musu da mafi karancin abin da suke bukata wajen gudanar da rayuwarsu inda ya ce: Shin wannan ba zalunci da kuma take hakkokin bil'adama ba ne. Shin a irin wannan yanayin bai kamata su ji kunyan maganar kare hakkokin bil'adama ba?

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da alkawarin da shugaban kasar Amurka ya yi a lokacin yakin neman zabe na rufe gidan yarin Guantanamo idan aka zabe da kuma rashin cika wannan alkawarin inda ya ce: Irin hare-haren da jiragen yakin Amurka marsa matuka suke kai wa al'ummar Pakistan da Afghanistan da sauran dubban zalunci da ta'addancin da suke yi a duniya, hakan lamari ne da ke nuni da hakikaninsu da kuma take hakkokin bil'adama da suke yi.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: Lalle mu muna karar Amurka da mafi yawa daga cikin gwamnatocin kasashen yammaci dangane da batun take hakkokin bil'adama, sannan kuma mun kai kararsu zuwa ga kotunan kwakwalan al'ummomin duniya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Al'ummar Iran, ta hanyar dogaro da Allah Madaukakin Sarki, za ta tsallake dukkanin matsalolin da aka kirkiro mata sannan kuma za ta kai ga manyan manufofinta.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da irin matsayin da al'ummar Qum suke da shi da kuma irin rawar da suka taka wajen tabbatar da nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran inda ya ce: Garin Qum a matsayinsa na cibiyar malaman Shi'a da na Musulunci, lalle ta kasance wata alama ta daukakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

 

1352707

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: