An yi wadannan kalamai ne a matsayin martani ga wani gangamin da Imam Qasim Khan ya jagoranta a birnin Houston, inda ya bukaci wasu shaguna mallakar musulmi da su daina sayar da kayayyaki irinsu naman alade da barasa, wadanda musulunci ya haramta. Gangamin ya haifar da cece-kuce na siyasa da kafafen yada labarai.
Mutanen da ke da alaka da masu tsatsauran ra'ayi a Amurka sun yi iƙirarin cewa Musulmi a jihar Texas na son hana Amirkawa cin naman alade da shan barasa.
A martanin da Greg Abbott ya yanke, Majalisar Hulda da Addinin Musulunci ta Amurka (CAIR) ta jaddada cewa, shari'ar Musulunci kamar sauran dokokin addini (Yahudanci da Katolika) ana amfani da su ne kawai a cikin al'amuran da suka shafi sirri da kuma na addini, kuma ba ta ci karo da dokokin Amurka ba.
Gwamnan Texas Greg Abbott mutum ne da ya yi fice a fagen siyasa da ya shahara da kalamansa kan batutuwan da suka shafi addini da tsaro kuma dan jam'iyyar Republican ne kuma ya taba rike mukamin gwamnan jihar Texas tun shekara ta 2015.
A baya gwamnan jihar Texas ya yi kokarin hana musulmi gina gida da masallaci a wani fili mai girman eka 400 a kusa da birnin Josephine na jihar Texas.
Kwanan nan gwamnan na Republican ya sanar a shafukan sada zumunta ta hanyar sake buga wani faifan bidiyo game da aikin: "Domin a fayyace, an haramta shari'ar Musulunci a Texas, kuma babu wani birni da aka yarda ya aiwatar da Shari'a."
A shekarar 2024, an gabatar da korafe-korafe 8,658 na nuna wariya ga musulmi, wanda ya karu da kashi 7.4 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2023. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa adadin wariyar launin fata ga musulmin Amurka ya kai kusan kashi 15 cikin dari.