IQNA

Fadada Alaka Tsakanin Iran da Afirka Ta Kudu A fagen Musulunci

11:19 - January 13, 2014
Lambar Labari: 1358291
Bangaren kasa da kasa, gwamnatocin kasashen Afirka ta kudu da kuma jamhuriyar muslunci ta Iran suna da kyakyawar alaka a dukkanin bangarori da hakan ya hada da bangaren al’adu da kuma musayar ilimi tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo daga bangaren yada labaransa na Afirka kan cewa, mai kula da karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Johannesburg ya bayyana cewa, gwamnatocin kasashen Afirka ta kudu da kuma jamhuriyar muslunci ta Iran suna da kyakyawar alaka a dukkanin bangarori da hakan ya hada da bangaren al’adu da kuma musayar ilimi tsakanin kasashen nasu.

Ya ci gaba da cewa tun zamani mai tsawo Musulunci ya fara shiga nahiyar Afirka, wanda hakan ke komawa tun daga lokacin da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka ya tura tawaga ta farko da ta fara yin hijira a cikin tarhin addinin Musulunci zuwa Habasha.

Kasashen Afirka na taka gagarumar rawa wajen bunkasa harkokin addinin muslunci fiye da kasashe da daman a larabawa, inda sukan fifita addinin a kan komai na sun a rayuwa tare yin kokari wajen kiyaye dokokin addinin a cikin lamurran siyasar kasashensu musamman ma kasashen da musulmi suke da rinjaye.

1353571

captcha