IQNA

Taron majalisun dokokin kungiyar kasashen Musulmi na 9 a Tehran

11:50 - February 20, 2014
Lambar Labari: 1377571
A jiya talata ce aka fara taron kungiyar majalisun dokokin kasashen musulmi karkashin kungiyar hada kan kasashen musulmi ta OIC a nan birnin Tehran. Taron na kwanaki biyu ya sami halattar shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen musulmi 30, mataimakan shuwagabannin majalisun dokoki 17 da kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa masu sanya ido a cikin kungiyar guda 15.

Taron na jiya talata dai ya sami halattar shugaban kasar Iran, dr Hassan Ruhani, shugaban majalisar dokokin kasar Iran da kuma alkalin alkalan kasar. A jawabinsa wajen bude taron Dr Hassan Ruhani, shugaban kasar Iran ya yi kira ga kasashen musulmi su hada kai, su kuma yi amfani da dimbin arzikin da Al..ya basu don samar da wani sauyi babba a duniya, wanda kuma zai bawa musulmi matsayin da ta dace da su a cikinta. 

Shugaban kungiyar majalusun dokokin kasashen musulmi na 8, wanda kuma shi ne shugaban majalisar dokokin kasar Sudan Fatihu Izzuddeen Mansur a cikin jawabinsa a taron na jiya, ya bayyana cewa yana daga cikin manufofin kafa majalisar, samarwa al-ummar Palsdinu yencinta da kuma hana yahudantar da lardin Palasdinu da aka mamaye.

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Dr Alin Larijani, wanda kuma ya karbi jagorancin kungiyar a matsayin shugabanta na 9, ya bukaci hadin kai tsakanin musulmi, don hana makiya ci gaba da jefa gaba da kiyyayya tsakaninsu, da kuma amfani da wasu masu kafirta musulmi don samar da fitinu a tsakaninsu.

A zaman kungiyar ta jiya dai shuwagabannin majalisun dodkoki na kasashen Afganistan, Suriya, Iraqi, Kuwait, Lebanon, Qatar, Niger, Omman, Emarat, Bangladesh, Yemen, Ivory Coast, Azarbajan, Jordan, Malasia da kuma  Sudan ne suka gabatar da jawabansu.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ce ta jagoranci kafa kungiya ta majalisun dokokin kasashen musulmi a shekara 1999 da nufin samar da hadin kai da kuma ya da arzikin da addinin Musulunci yake da shi a bangarorin rayuwar bil’adama daban daban. Za’a kammala taron a yau laraba.

1377498

Abubuwan Da Ya Shafa: Larijani
captcha