
Jaridar Colorado Times ta kasar Amurka a cikin wani sabon rahoto da ta fitar, ta bayyana tare da tabbatar da zurfin al’amarin na kyamar addinin Islama a cikin al’ummar kasar Amurka, wanda a cewar tsohon jami’in hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Jimmy Haas, yanzu ba takaitacciyar halayya ko halayya ta daidaikun mutane ba, sai dai ya zama hadaddiyar tsarin cibiyoyi da hukumomin tsaro, kafafen yada labarai da ‘yan siyasa ke gudanarwa.
Haas ya bayyana cewa kiyayya ga musulmi ta zama haramtacciyar kiyayya a Amurka, inda harzuka masu tayar da kayar baya a kan Musulunci da musulmi ke tafiya ba tare da an hukunta su ba, yayin da duk wani cin zarafi da ake yi wa wasu addinai ko kabilu yana fuskantar hukunci mai tsanani.
Rahoton ya gano cewa tushen wannan lamari ya samo asali ne tun bayan 11 ga watan Satumba, lokacin da aka yi amfani da tsoron Musulunci a matsayin wani makami na karfafa ikon cikin gida da tabbatar da munanan manufofin kasashen waje. Rahoton ya bayyana cewa, manyan cibiyoyin tsaro da kafofin yada labarai sun taka rawa wajen bata sunan addinin Musulunci.
Rahoton ya kuma yi nuni da yadda hare-haren da ake kai wa masallatai a Amurka ke kara ta'azzara, da yadda hukumomi suka ki ba da izinin gina sabbin masallatai.
A cikin wannan yanayi, rahoton ya nakalto Haas na cewa fitattun ‘yan siyasa irin su Sanata Ted Cruz, sun yi kalaman nuna kyama ga musulmi ba tare da wani hukunci na shari’a ba.
A karshe rahoton ya jaddada cewa kawancen Amurka da Isra'ila ya taka rawar gani wajen rura wutar wannan lamari ta hanyar kafafen yada labarai da na siyasa da ke bayyana Musulunci a matsayin wata barazana ta wanzuwa.