Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam Web cewa, a cikin wannan makon da muke cikin ne aka buga tare da wani kamus na kalmomin kur'ani mai tsarki a kasar Moroco da nufin kara habbaka harkokin karatun kur'ani tare da sanin ma'anoninsa a tsakanin al'ummar kasar musamman ma daliban addinin musulunci da kuma amsu koyon karatun kur'ani a makarantu.
A wani labarin kuma na daban, masu zanga zanga a kasar Maroko sun mamaye titunan garin Jebel Bou Mehraz domin yin Allah wadai da cin zarafin fursunonin siyasa da ake tsare da su kasar.
Masu zanga zangar sun yi tir da azabtar da fursunonin siyasa da suka ce yan sandan kasar suna yi, sun kuma bukaci a sallami fursunoni ba tare da bata lokaci ba. A yan watannin nan dai jamaa suna gudanar da gangami a kai a kai a kasar ta Maroko domin kokawa dangane da cin hanci da rashawa da cin zarafin jamaa da kuma talauci da ya yi wa mutane katutu.
A wata kuriar jin raayin jamaa da aka gudanar a watan Yuli alummar kasar Maroko sun amince da sabon kundin tsarin mulki wanda ya rage ikon Sarki Muhammad na IV amma mutanen kasar suna bukatar a magance musu matsalolin da suke fama da su kamar talauci rashin aikin yi.