Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labaransa a nahiyar Afirka cewa, a cikin wannan mako an gudanar da wani zama da nufin karfafa hadin kan al'ummar musulmi a kasar Saliyo bisa la'akari da matsalolin da ake nufin haddasawa tsakanin mabiya addinin muslunci da kuma kiristocia cikin wasu kasashe da ke cikin nahiyar kamar jamhuriyar afirka ta tsakiya.
Taron wanda ofishin kula da harkokin al'adu na jamhuriyar musulunci ta Iran ya shiriya, ya samu halartar malamai da kuma daliban addini daga bangaren mabiya tafarkin ahlul bait da kuma 'yan sunna na kasar, kuma dukaknin bangarorin biyu sun nuna jin dadinsu da wannan kokari na hada kan musulmi, domin su fuskanci makircin da ake shira musu domin rarraba su.
Kasar Saliyo dai na daga cikin kasashe da suke samun ci gaba matuka ta fuskar addinin muslunci, inda ake ci gaba da bude makarantun addini da suka hada da na karatu da kuma harder kur'ani mai tsarki.