IQNA

Daruruwan Musulmi Sun Yi Zanga-Zangar La'antar Hollande A Ziyararsa Bangui

23:26 - March 02, 2014
Lambar Labari: 1382059
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Afirka ta tsakiya sun ce wasu daruruwan musulmi sun yi zanga-angar nuna rashin amincewarsu da ziyarar da shugaban kasar Faransa Francios Hollande ya kai kasarsu tare da bayyana hakan a matsayin wani abu maras amfai gare su

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Afrik cewa, daruruwan musulmi sun yi zanga-angar nuna rashin amincewarsu da ziyarar da shugaban kasar Faransa Francios Hollande ya kai kasarsu a cikin wanann mako, inda suka ce Faransa tana da hannu a kisan kiyashin da ake yi musu.

Shugaban kasar Faransa Francios Hollande ya kai wata ziyara ta yini guda a yau a birnin Bangui na jamhuriyar Afieka ta tsakiya, inda ya gana da jami'an gwamnatin rikon kwayar kasar da kuma sojojin Faransa da suke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya.
Kamfanin dilalncin labaran kasar ta Faransa ya bayar da rahoton cewa, Francios Hollande ya isa birnin Bangui ne bayan da ya bar birnin Abuja na tarayyar Najeriya a yau, inda ya halarci shugabannin kasashen Afirka kan tsaro da yaki da ta'addanci da kuma ci gaban Afirka, wanda aka gudanar lokacin bukukuwan cikar Najeriya shekaru 100 da dunkulewa kudu da arewa.
Hollande ya gana da shugabar rikon kwaryar jamhuriyar Afirka ta tsakiya Catharine Samba-Panza, kamar yadda ya gana da sojojin Faransa da ke kasar, inda ya karfafa gwiwarsu kan aikin da suke gudanarwa na wanzar da zaman lafiya a kasar.
1381244

Abubuwan Da Ya Shafa: Bangui
captcha