Babban taron majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kudurin da kasashen Faransa da Saudiyya suka gabatar, wanda ya amince da kuma goyon bayan sanarwar da aka cimma a birnin New York na kasar Amurka kan batun warware matsalar Falasdinu cikin lumana da kuma aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
Kuri'u 142 ne suka amince da daftarin kudurin kafa kasar Falasdinu, kuri'u 12 na adawa da shi, sannan 10 suka ki kada kuri’a.
Bayanin daftarin kudurin ya yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaiwa kan fararen hula a zirin Gaza, da kayayyakin more rayuwa na fararen hula, da kewaye da kuma yunwa, tare da jaddada cewa, dole ne a aiwatar da aikin maido da tsarin zaman lafiya a yankunan Falasdinu ba tare da kasancewar kungiyar Hamas ba, wanda shi ne tubalin al'ummar Gazan sama da miliyan biyu.
Kudurin ya kuma jaddada cewa dole ne a kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza a yanzu.
Kuri'ar na yau na zuwa ne gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da Riyadh da Paris za su jagoranta a ranar 22 ga watan Satumba a birnin New York, inda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alkawarin amincewa da kasar Falasdinu a hukumance.
https://iqna.ir/fa/news/4304644