IQNA

Wani Yaro Dan Shekaru 5 Da Haihuwa Ya Hardace Kur'ani Mai Tsarki A Aljeriya

19:46 - March 10, 2014
Lambar Labari: 1385548
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankula a wasu kafofin yada labarai a kasar Aljeriya da ma wasu daga cikin kasashen larabawa shi ne samun yaro dan shekaru biyar a kasar wanda ya hardace dukkanin kur'ani mai tsarki. Kamfanin dillancin lab

aran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na egyp.com cewa, Abdulrahman Farih dan shekaru 5 da haihuwa dan kasar Aljeriya ya hardace kur'ani mai tsarki baki daya, tare da karanta shi da salon kir'a ta tartili, kuma lamarinsa ya dauki hankula matuka a kasashen musulmi da dama da na larabawa.

Tashar talabijin ta MBC ta bayar da cikakken rahoto kan rayuwarsa da kuma yadda ya tashi, inda ya kasance ya samu jinkirin magana bayan haihuwarsa har tsawon shekaru biyu ba tare da bakinsa ya bude ba, amma daga lokacin da bakinsa ya bude ya fara ne da karatun surat Kahf, kuma yana karnta ta ba tare da wata matsala ba.

Bayanin ya kara da cewa ya kara da cewa a zantawar da aka yi da mahaifiyarsa kan batun nasa, ta bayyana cewa tun a lokacin da take dauke da shia  ciki, ta kasance tana karanta surat Kahf a kowace rana, wanda kuma ko shakka babu hakan ya yi tasiri wajen samun natsuwar abin da ke cikin cikinta.

1384655

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeriya
captcha