IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Na Shirin Fitar Da Musulmi Daga Afirka Ta Tsakiya Don Kare Su

16:56 - April 10, 2014
1
Lambar Labari: 1392784
Bangaren kasa da kasa, Majalisar dinkin uniya na shirin kwashe musulmi daga kasar Afirka ta tsakiya da nufin taimawa wajen kare su daga kisan kiyashin kiristoci, maimakon taimaka musu ta hanyar dakatar da kisan da ake yi musu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kwamitin tsaro na duba yiyuwar aikewa da dakarun samarda zaman lafiya a jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya. Kasar Faransa ce dai ta mika wanan bukata ga kwamitin, inda take neman a aike da dakarun samarda zaman lafiya a Afrika ta Tsakiyar wace rikicin addini dana kabilanci ya daidaita.
Membobin kwamitin dake haduwa yau zasu duba wanan batun domin amuncewa da tura dakarun ko kuma akatsin haka. Idan dai har wanan bukatar Faransa ta samu rinjaye a kwamitin to za’a aikewa da dakarun samarda zaman lafiya dubu 11, da kuma ‘yan sanda dubu da dari takwas a jamhuriya Afrika ta Tsakiyar a watan satumber wanan shekara.   
Rahotanni daga kasar Afirka ta tsakiya sun bayyana cewar tawagar farko na dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen Turai sun isa birnin Bangui babban birnin Afirka ta tsakiya don tabbatar da zaman lafiya da kuma kawo karshen rikicin da ke faruwa a can.
Kamfanin dillancin labaran ya jiyo kakakin sojojin Faransa Francois Guillermet yana tabbatar da isar tawagar farko na sojojin Tarayyar Turan inda ya ce tuni har wasu daga cikinsu sun fara yawon sintiri a babban birnin (Bangui) don tabbatar da zaman lafiya da kuma horar da sojojin kasar a cewarsa.
A bangare guda kuma ‘yan sanda a kasar Afirka ta tsakiyan sun bayyana cewar wasu mutane 30 mafiya yawansu fararen hula sun rasa rayukansu sakamakon wani sabon rikici da ya barke tsakanin ‘yan bangan Kiristoci da musulman kasar.

1392328

Abubuwan Da Ya Shafa: Bangui
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 1
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Gambo Ngudel
6
2
Ya kamata a barsu a nemi hanyan yin sulhu ba wai a kwashe su daga kasan shine taimako ba. Idan har an yi haka ya nuna akwai wani abu kenan. Don haka idan har ana da niyan yin taimako ayi kokarin neman yadda zaayi don a sami zaman lafiya a kasan.
captcha