Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo quran.univ.sd cewa, a cikin makon da ya gabata ne aka gabatar da taruka na mayar da babbar cibiyar bincike kan ayyukan kur’ani da ilmominsa da ke kasar Sudan zuwa babbar jami’ar koyar da ilmomin kur’ani domin amfanin alumma.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan aiki ya gudana bayan namijin kokarin da gwamnatin kasar ta yi na ganin cewa ta samar da wata jami’a wadda za ta kebanci wannan gagarumin aiki, wanda kuma wannan cibiya wadda ta nisa wajen gudanar da ayyukan da suka shafi kur’ani ta yaye dubban dalibai da suka cancanci su zama malamai ta wanann fuska, akan haka aka yanke shawar mayar da cibiyar ta zama jami’a.
A wani labarin na daban kuma an bayyana cewa Sojojin kasar Sudan Sun Samu nasarar tsarkake yankuna da dama daga 'yan tawaye a yankin Kurdufan ta kudu. Kakakin Sojan Sudan Sawarimi Khalid Sa'ad ya bayyana cewa Dakarun kasar sun samu nasarar tsarkake yankuna guda 12 daga hanun 'yan tawaye a gabacin Darfur ta kudu inda yace yanzu haka babu wasu 'yan tawaye a wadannan yankuna.
Kakakin ya kara da cewa Dakarun kasar za su ci gaba da ayyukansu har sai sun tsarkake dukkanin yankunan da 'yan tawaye suka kafa sansaninsu a can, tun a watan yuli ne na shekarar 2011 aka fara samun matsalar 'yan tawaye a Kurdufan ta kudu dake kudancin Sudan.
1395153