IQNA

Taro Kan Matsayin Mata A Mahangar Addinin Musulunci A Kasar Ethiopia

15:59 - April 22, 2014
Lambar Labari: 1398667
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro a kasar Ethiopia dangane da matsayin mata a cikin addinin muslunci da kuma yadda musulunci ya ba su matsayi na musamman a cikin al’umma da kuma tarbiyantar da ita.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da wani zaman taro a kasar Ethiopia dangane da matsayin mata a cikin addinin muslunci da kuma yadda musulunci ya ba su matsayi na musamman a cikin al’umma da kuma tarbiyantar da ita bisasahihin tafarki.
A wani labarin na daban kuma Wasu yan bindiga sun kashe mutane 9, sun kuma jiwa mutatne 7 rauni a cikin wata babbar mota a kasar Ethiopia a yau Laraba, majiyar gwamnatin kasar Ethiopia ta bayyana cewa mutane 25 ne a cikin motar a lokacinda yan bindigan suka kawo mata hari.
Majiyar ta kara da cewa gwamnati tana bincke don gano wadanda suka kai harin, amma har yanzun babu wanda, ko kuma wata kungiya da ake tuhuma da kai harin, an kai harin ne a yankin Benishangul kilomita 400 arewa maso gabaci birnin Adis Ababa.
Majiyar dai ta nisanta hasashen cewa harin na kungiyar Alshabab ta kasar Somalia ce don ganin nisan yankin daga kaniya da kasar.
1397779

Abubuwan Da Ya Shafa: ethiopia
captcha