IQNA

Musulmin Afirka Ta Tsakiya Sun Nuna Rashin Gamsuwa Da Matakan Gwamnati

19:14 - June 02, 2014
Lambar Labari: 1413800
Bangaren kasa da kasa, shugabar rikon kwarya ta kasar A frika ta tsakiya ta bayyana damuwarta akan halin da rashin tsaron kasar ke ciki. Shugaba Kathrine Panza ta fada a yau alhamis cewa; Duk da ci gaba da aka samu na azo a gani ta fuskar tsaro, sai dai har yanzu kasar tana ci gaba da fuskantar matsaloli. Shugaba Panza wacce a halin yanzu ta ke ziyara a wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa.  duk da cewa a cikin wannan shekara ta 2014 an yi kokari wajen tabbatar da tsaro, sai dai babu wani gagarumin sauyi na azo a gani da aka samu. Bugu da kari shugaba Panza ta ce ta je kasar Congo Brazeville ne domin tattauanwa da shugaba Saso Angiso wanda shi ne mai shiga tsakani domin gano bakin zaren yadda za a warware matsalar kasarta da kuma ta yankin.
Kwana daya bayan da shugabar gwamnatin rikon kwarya ta kasar, Catherine Panza ta yi furuci da cewa, har yanzu babu cikakken zaman lafiya a kasar. Fada da musulmi da su ke tsiraru a cikin kasar Afirka ta tsakiya ya tsananta a cikin watannin bayan nan, tare kuma da tilastawa wasu dubbai yin hijira zuwa kasashen mawkabata
An sami dawowar kwanciyar hankali na azo a gani a baban birnin kasar Afirka ta tsakiya, Bongui bayan kwana na rikici. Da safiyar yau asabar an sami nutsuwa akan titunan babban birnin kasar ta Afirka ta tsakiya. A jiya juma’a dai wasu kiristoci masu tsattsauran ra’ayi sun kai hari a kan wani masallacin da ke babban birnin kasar. A cikin unguwar Bk5 da mazaunanta musulmi ne sun kafa shinge-shinge domin kare kansu daga hare-haren da ake kai musu. Da safiyar yau asabar an ga jiragen soja masu saukar angulu mallakin Faransa suna shawagi a saman babban birnin kasar Bongui.
1412916

Abubuwan Da Ya Shafa: CAR
captcha