IQNA

Fatawar Ayatollah Sistani Na Bayyana Halin Da Ake Ciki A Iraki

15:38 - June 16, 2014
Lambar Labari: 1418366
Bangaren kasa da kasa, fatawar da babban malamin addinin muslunci a Iraki Ayatollah Sistani ya bayar domin yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta alkaida a kasar hakan ya nuna irin halin hadarin da ake ciki a kasar ne.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa cibiyoyin Musulunci na Shi’a da Sunna a kasar Iraki suna ci gaba da sanar da goyon bayansu ga matakin da manyan malaman Shi’a da na Sunna na kasar Iraki suka dauka na shelanta jihadi a kan ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh masu kafirta musulmi da suka kame wasu yankuna nan kasar Irakin.
Rahotanni daga kasar Irakin sun ce a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da cibiyoyin Shi’a da Sunna na lardin Babu na kasar suka fitar a jiya Lahadi sun ce bisa la’akari da hare-haren da ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh da take samun goyon bayan sauran gyauron magoya bayan  tsohuwar gwamnatin kasar da nufin rarraba kasar Iraki da haifar da fitina a tsakanin al’ummar kasar, muna sanar da goyon bayanmu ga fatawoyin da malaman Shi’a da na Sunna na kasar Irakin suka fitar na fada  da ‘yan kungiyar ta Da’esh.
Har ila yau sanarwar ta kara da cewa muna nuna goyon bayanmu a zance da kuma a aikace sannan kuma za mu shiga cikin sahun fada da makiyan da muka yi tarayya kansu; kamar yadda kuma muke sanar da hadin kanmu waje guda  a matsayinmu na ‘yan Shia da Sunna wajen fada da wannan makirci na rarraba kasar Iraki da haifar da fitina a tsakanin ‘yan kasar.
Babban malamin addinin Musulunci a kasar Iraki Ayatullahi Aliyu Sistani ya shelanta jihadi kan ‘yan ta’adda da nufin kare kasar daga mamayar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi.
A hudubar sallar juma’arsa a birnin Karbala na kasar Iraki Sheikh Abdul-Mahdi Al-Karbala’i wakilin babban malamin addinin Musulunci a Iraki Ayatullahi Sistani ya bayyana cewa; Ayatullahi Aliyu Sistani ya bukaci dukkanin al’ummar Iraki da su daura damara tare da sabar makamai domin yakar ‘yan ta’adda da nufin kare kasar Iraki.
Sheikh Karbala’i ya kara da cewa; Babban hatsari yana barazana ga kasar Iraki don haka wajibi ne a kan mutanen da suke da damar daukar makami su shiga cikin sahun jami’an tsaron Iraki domin kare kasar, kuma duk wanda ya mutum ya yi shahada a matsayin shahidi.
1417625

Abubuwan Da Ya Shafa: Iraq
captcha