Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanagizo cewa, rahotonni daga Iraki suna tabbatar da cewar jami’an tsaron kasar da taimakon jama’ar Iraki da suka sabi makamai domin kare kasarsu daga ayyukan ta’addanci sun samu nasarar ‘yantar da wasu yankunan kasar daga mamayar ‘yan ta’addan kungiyar Daular Musulunci a Iraki da Sham ta Da’ish tare da halaka da dama daga cikin ‘yan ta’addan.
Majiyar rundunar sojin Iraki a jiya Asabar ta tabbatar da cewa; Jami’an tsaron kasar da suka hada da sojoji da ‘yan sanda gami da jama’ar gari da suka sabi makamai domin kare kasarsu daga mamayar ‘yan ta’adda musamman dakarun sa-kai karkashin jagorancin shugabannin kabilun Larabawan kasar suna ci gaba da fafatawa da gungun ‘yan ta’adda a lardunan Silahuddin, Anbar da Diyala da suke arewaci da yammaci da kuma gabashin kasar Iraki.
A tsawon kwanaki biyar da aka kwashe ana gumurzu a lardunan da suke karkashin mamayar ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish; Jami’an tsaron Iraki da dakarun sa-kai da suke tallafa musu sun samu nasarar ‘yantar da muhimman yankuna a lardunan uku tare da halaka daruruwan ‘yan ta’adda da jikkata wasu adadi masu tarin yawa gami da tarwatsa motocin yaki masu dauke da manyan makamai da matsakaita da ‘yan ta’addan suke amfani da su wajen kai hare-haren mamaya kan yankunan kasar.
Tun a ranar Talatar da ta gabata ce gungun ‘yan ta’adda da suka hada da magoya bayan tsohuwar jam’iyyar Ba’as ta Saddam Husain dan kama karya da wasu kungiyoyin addini masu dauke da akidar kafirta musulmi karkashin jagorancin kungiyar ta’addanci ta Daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish suka kaddamar da hare-haren mamaya a wasu garuruwan lardunan kasar Iraki tare da fara aiwatar da barna a bayan kasa, inda ko a jiya Asabar tashar talabijin din Al-Irakiyya ta kasar Iraki ta watsa labarin cewa; ‘Yan kungiyar Da’ish sun kashe mutane 12 ciki har da babban limamin masallacin juma’ar Al-Asra’u da ke garin Mosel Sheikh Muhammad Al-Mansuri tare da giciye gawarsa saboda sun ki yin mubaya’a ga kungiyar. Sannan a halin yanzu haka manyan limaman masallatan juma’a fiye da 34 da suka fito daga sassa daban daban na lardunan da ‘yan ta’addan Da’ish suka mamaye kuma mafi yawansu mabiya mazhabar sunnah sun tsere zuwa garin Arbil da ke karkashin yankin Kurdawa mai cin kwarya-kwaryar gashin kai a kasar ta Iraki domin tsira da rayuwarsu.
A gefe guda kuma kungiyar malaman addinin Musulunci ta kasar Iraki ta mabiya mazhabar Ahlus-Sunna waj- Jama’a a jiya Asabar ita ma ta fitar da fatawar shelanta jihadi kan ‘yan ta’addan Da’ish da dukkanin masu goya musu baya a kasar. Kungiyar malaman ta jaddada yin kira ga al’ummar Iraki da su dauki makami su shiga cikin sahun jami’an tsaron kasar domin kare addininsu da mutuncin kasarsu daga mabarnata sojojin haya.
1418011