IQNA

A Gobe za A Dauki Azumi A Kasashen Larabawa Da Dama

20:16 - June 29, 2014
Lambar Labari: 1423902
Bangaren kasa d akasa, kasashen larabawa da dama da kuma wasu daga ckin kasashen musulmi sun sanar da gobe a matsayin ranar da za sy fara gudar da azumin watan Ramadan mai albarka.

al'umma a jamhuriya musulinci ta Iran zasu dauki azumi Lahadi idan Allah ya kai bayan an hango jinjirin watan na Ramalana dazu a wasu sassan kasar.   Hango jijinrin watan na a matsayin ranar karshe ta watan Sha’aban sannan kuma gobe Lahadi a matsayin ranar farko na watan Ramalana na wannan shekara. 

Yanzu haka dai dama tunda farko kasashen da dama sun sanar da daukan azumin a gobe lahadi idan Allah ya kai mu. A tarayya Najeriya dai yau al'umma musulmai sun wuni da Azumin farko bayan sanarda sinkayen jinjirin watan jiyya, koda yake wasu rahotanni sun ce jama'a da dama basu daukin azumin ba a yau, saboda basu ji sanarwar fara azumin ba.

Tun daga cikin kasashen da suka sanar da ranar Lahadi a matsayin ranar farko ta watan Ramadan, akwai Iran, Sadiyyah, Masar, Palastinu, Jordan, Iraki, Somalia, Syria, Indonesia da kuma Malazia, yayin da wasu kasashen kuma da suka sanar da ganin wata a ranar Juma'a suka tashi da azumi a jiya Asabar, daga ciki kuwa har da kasashen Yemen, Turkiya da kuma Najeriya da ma wasu daga cikin kasashen yankin.
1423071

Abubuwan Da Ya Shafa: ramadan
captcha