Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Irak Alkanun cewa, Sheikh Khalid Mullah shugaban majalisar malaman Iraki ya ce majalisar tana yin Allawadai da ayyukan ta'addancin da kungiyar ISIL take aikatawa da sunan addinin muslunci da kuma rusa masallatai da kabrukan bayin Allah waliyayyai da sunan hana shirka.
Ma’aikatar tsaron kasar Iraki ta yi karin haske kan irin nasarorin da dakarun kasar suke ci gaba da samu a kan ‘yan kungiyar ‘yan ta’addan nan ta Da’esh ko ISIS da ta mamaye wasu yankuna na kasar inda ta sanar da cewa a jiya sojojin sun sami nasarar ruguza wasu motoci guda hudu da ke dauke da ‘yan ta’addan a yankin Jarf Sakhar da ke lardin Babul inda suka hallaka dukkanin mutanen da suke ciki da aka ce akwai wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’addan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a, ma’aikatar tsaron ta Iraki ta ce jiragen saman yakin Irakin ne suka tarwatsa wadannan motoci guda hudu da baya ga ‘yan ta’addan da suke ciki har ila yau kuma akwai wasu manyan makamai a cikinsu da ake shiri tafiya da su wasu yankuna na lardin.
Cikin ‘yan kwanakin nan dai sojojin na Iraki sun ba da muhimmanci kan wannan lardi na Babul da ‘yan ta’addan suka jibge wani adadi mai yawa na mayaka da makamansu ta yadda ya zuwa yanzu dai an sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na su.
A bangarori daban-daban na kasar Irakin ma dai lamarin haka yake inda sojojin suke ci gaba da samun nasarori kan ‘yan ta’addan na kungiyar Da’esh da suke samun goyon bayan wasu kasashen larabawa musamman kasar Saudiyya.
'Yan ta'addan kungiyar ISIL sun yanka limamin masallacin Annabi Yunus (AS) da ke birnin Mausil a arewacin kasar Iraki, bayan da yaki ya mika musu masallacin, da kuma kin bayar da fatawar korar kiristoci daga birnin.
1426143